Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya
A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula, musamman kananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki.
Wadannan kalamai sun zo ne a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar, inda aka yi karin haske kan rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, wanda ya yi sanadiyyar raba mutane kimanin miliyan 12 da matsugunan su.
Yakin dai ya kawo cikas wajen kai agajin jin kai, ya haifar da karancin abinci da kuma ta’azzara yunwa, in ji Mohamed Ibn Chambas, shugaban kwamitin Tarayyar Afirka kan Sudan.