Kungiyar gwagwramayar Falasdinawa ta yi Allah wadai da Sanya sunan kungiyar Ansarullahi ta Yemen da Amurka ta yi cikin jerin kungiyoyin ta’addanci
Kungiyar Mujahidan Falasdinawan ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na sanya kungiyar Ansarullahi a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda, saboda goyon bayan da take baiwa al’ummar Falastinu a Gaza. Kungiyar dai ta dauki wannan mataki a matsayin wani mummunan hari kan al’ummar Yemen ‘yan uwan juna masu kare kimar bil’adama.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta jaddada cewa: Wannan mataki na rashin adalci na nuni da wani sabon matakin kare masalahar gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya, wanda ya ba ta damar ci gaba da aikata laifukan da take aikatawa kan al’ummar Falastinu. Ta yi nuni da cewa, wannan na kara matsayin kara daukar Amurka babbar abokiyar kawancen ‘yan mamayar Isra’ila ce cikin laifuffukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da suka hada da kokarin shafe wata al’umma daga kan doron kasa da aiwatar da kisan kiyashi a Zirin Gaza.