Kungiyar Kwadago Mafi Girma A Canada Zata Hana Makamai Isa HKI

Kungiyar kwadago mafi girma a kasar Canada (CLC) ta sha alwashin hana aikawa HKI makamai daga kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta

Kungiyar kwadago mafi girma a kasar Canada (CLC) ta sha alwashin hana aikawa HKI makamai daga kasar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shuwagabannin kungiyar suna cewa, ma’aikatan kwadago a kasar ba zasu sake taba makami wanda za’a aika shi HKI ba, saboda yahudawan Sahyoniya suna amfani da makaman don kissan Falasdinawa a Gaza.

Labarin ya kara da cewa, kungiyar (CLC) tana wakiltan ma’aikata kimani miliyon 3 a kasar. Kungiyar a wani bayanin da ta fitar ta bayyana cewa tana goyon bayan al-ummar Falasdinu a gwagwarmayan da suke yi da HKI, suna kuma goyon bayan ma’aikata a kasar Falasdinu.

Bayanin wanda suka fitar a ranar 28 ga watan Octoba ya kara da cewa, kungiyar tana goyon bayan wadanda suke gwagwarmayar tabbatar da zaman lafiya a duniya, suke kuma neman adalci. Daga karshe ta yi kira ga kasashen duniya su yi biyayya ga dokokin kasa da kasa.

CLC ta ce zata yi kokarin ganin daga yanzun kuma gwamnatin kasar ba zata aika makamai zuwa kasar Falasdinu daga kasar ba. Haka ma, ba zata amince a yi amfani da kasar don wucewa da makamai zuwa HKI ba.

Daga karshe ta bayyana cewa, Ottawa ta kiyaye dokokin kare hakkin bil’adama da kuma na isar da kayakin jinkai zuwa duk inda mabukata suke a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted