Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana cewa: Abin da aka cimma na yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba kyauta ce daga kowa ba
Kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu ta bayyana cewa: Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da makiya yahudawan sahayoniyya ba kyauta ce daga kowa ba.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar da safiyar yau Alhamis din nan, kungiyar Jihadul -Islami ta kara da cewa: Ko da yake ba su musanta yunkurin kasashen Larabawa da na kasa da kasa ba, amma suna jaddada gagarumin sadaukarwar da al’ummar Falastinu suka yi da kuma jajircewa da dogewa wajen kalubalantar makiyansu a fagen daga.
Bayanin ya ci gaba da cewa: A wannan lokaci na tarihi, al’ummar Falasdinu ba za su manta da shahidai masu girma da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin gwagwarmaya ta ci gaba da wanzuwa ba da kuma isa ga wannan muhimmin mataki, inda za a iya kammala abin da aka amince da shi na tilasta wa makiya dakatar da kai farmakin.