Jami’a a kungiyar ta kare hakkin bil’adama Sarah Basi ta bayyana a jiya Litinin cewa; Cikin ganganci ne ‘yan mamaya suke hana a shigar da kayan agaji cikin yankin Gaza, tare da yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan sahayoniyar da su bude hanyoyin shigar da kayan agajin.
Har ila yau Kungiyar ta yi kira ga Amurka da ta kawo karshen bai wa Isra’ila makamai.
Wannan kiran na kungiyar kare hakkin bil’adama yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu kungiyoyin ‘yan sahayoniya masu zurfin tsaurin ra’ayi suke yin kira da a kara matsin lamba a hare-hren da ake kai wa Gaza.
Minitan kudi na HKI Bezalel Yoel Smotrich ya bayyana cewa; Ko da yarda, ko babu yardar Amurka za su kai wa yankin Rafah hari.
Shi ma Fira minista Netenyahu ya fadi cewa; sun riga sun yanke hukuncin kai wa yankin na Rafah hari.
A cikin yankin Rafah ne dai mafi yawancin Falasdinawan da aka rusawa gidajen a sauran yankunan Gaza, su ka sami mafaka.