Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Suka Kai Kan Kasar Siriya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullahi ta fitar ta ce: Tana jaddada tofin Allah tsine da yin Allah wadai da zaluncin yahudawan sahayoniyya da suka addabi kasar Siriya a wani mummunan hari da suka kai kan yankunan kasar, tare da fakewa da munanan kalamai da take-take na aiwatar da ayyukanta na fadadawa da wargaza kasar Siriya da nufin rusa hadin kan kasar da kuma haifar da fitina a tsakanin al’ummarta.”

Kungiyar ta kuma jaddada cewa: Wannan wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya wani yunkuri ne karara na gurgunta zaman lafiyar kasar Siriya da raunana karfinta, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a kan kasar Lebanon da zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments