Kungiyar Hizbullahi Ta Kai Hare-Hare Har Sau 51 Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Rana Guda

A cikin hare-haren mayar da martani kan haramtacciyar kasar Isra’ila kungiyar Hizbullahi ta kai hare-hare har sau 51 a rana guda kan Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar

A cikin hare-haren mayar da martani kan haramtacciyar kasar Isra’ila kungiyar Hizbullahi ta kai hare-hare har sau 51 a rana guda kan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da takaitaccen bayani kan ayyukanta na yau da kullun musamman kai hare-haren daukan fansa kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a jiya Lahadi, wanda ake yi wa kallon a matsayin daya daga cikin mafi girman hare-haren da a kai wa ‘yan mamayar sahayoniyya a cikin yini guda tun bayan fara yakin ambaliyar Al-Aqsa.

Kafar yada labaran kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: A ranar Lahadi 24 ga watan Nuwamba, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da sanarwar soji ta mayar da martani har sau 51 dangane da hare-haren da suka kai kan makiya yahudawan sahayoniyya da suka yi yunkurin tsallaka kan iyakokin kasar Lebanon da ta bangaren Falasdinu da kuma dakile jiragen saman yakinsu da kuma jiragen sama  marasa matuka ciki, da kuma hare-haren da suka kai kan wurare, sansanoni da ake jibge sojojin sahayoniyya, baya ga kai farmaki kan matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke arewaci da cikin zurfin Falasdinu da aka mamaye.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments