Search
Close this search box.

Hizbullah Ta Tarwatsa Wasu Na’urorin Ayyukan Sojin Isra’ila

Kungiyar Hizbullah ta nuna faifan bidiyon yadda ta kai hare-hare kan wuraren na’urorin sojin h.k.Isra’ila a Al-Summaqa da Ramiya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta

Kungiyar Hizbullah ta nuna faifan bidiyon yadda ta kai hare-hare kan wuraren na’urorin sojin h.k.Isra’ila a Al-Summaqa da Ramiya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta wallafa faifan bidiyon farmakin da ta kai kan kayan aikin fasaha da na leken asirin rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wuraren Al-Summaqa da Ramiya.

Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa, ta kai hari kan yankin Ruwaisat Al-Alam da ke tsaunin Kafur Shuba da ke kasar Lebanon da aka mamaye da makami mai linzami, sannan kuma ta kai hari kan yankin Al-Malikiyah da makamai masu linzami, wadanda hare-haren biyu suka tarwatsa na’urorin sojojin na haramtacciyar kasar Isra’ila.

A wani labarin kuma, kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa, ta kai hari a wani wuri da aka jibge sojojin mamaya a kusa da Hanita da makamai masu linzami, kuma harin ya samu daidai yadda aka tsaita shi.

Kamar yadda a jiya litinin mayakan kungiyar Hizbullah suka ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da aka jibge sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a daura da kan iyakar kudancin kasar Lebanon da makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments