Majiyoyin Turai sun bayyana cewa: Martanin baya-bayan nan na kungiyar Hizbullah ya haifar da hasarar rayuka da jikkata da dama a haramtacciyar kasar Isra’ila
Majiyoyin tsaron Turai sun bayyanawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Hare-haren da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kaddamar kan sashi na 8200 a Glilot da kuma sansanin Ein Shemer sun janyo munanan hasarori ga haramtacciyar kasar Isra’ila.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa: Hare-haren sun yi sanadiyyar halakar da dama da kuma jikkata musamman a sashin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na sashin mai lamba 8200, wanda wadanda suka jikkata suka kai yahudawan sahayoniyya 74.
Majiyoyin sun kara da cewa: Adadin wadanda suka mutu a Glilot da Ein Shemer ya kai yahudawa 22, kuma wadanda suka jikkata sun haura 70.