Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba
Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da barazanar kai hari kan filin jirgin saman Lebanon da sauran muhimman wuraren kasar ba.
Sheikh Damoush ya jaddada a cikin hudubarsa ta Juma’a cewa “ya zama wajibi gwamnati ta magance matsalar jiragen Iran zuwa kasar Lebanon, domin wannan batu na farko da na karshe yana da alaka ne da ‘yancin kai da kuma martabar kasar Lebanon, kuma hakan na nuni da kwace ‘yancin matakin da kasar Lebanon ta dauka. Saboda hana saukar jiragen saman Iran a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Beirut wani mataki ne na haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka, kuma hakan wani tsoma baki ne a alakar kasa da kasa ta Lebanon, kuma hakan zai bude kofar jerin bukatu da gindaya sharuddan kan batun jigilar jiragen saman Iran, kuma ba a san inda za su kare ba, sabanin muradun Lebanon da al’ummar kasar.
A wani labarin kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Zartarwar kungiyar Hizbullah, Sheikh Ali Damoush, ya tabbatar da cewa: An gayyace su don halartar jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, wannan fitaccen shugaba mai girman tarihi, a wani yanayi na musamman, mai tarihi da wayewa.