A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu.
A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka nan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila zata saki fursunonin Falasdinawa 445daga cikinmazauna Gaza wadanda aka kama su bayan ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.
Fursunonin Isra’ila shida da za a sako a ranar Asabar din nan, za a kara da fursunoni goma sha tara masu rai da kuma matattun yahudawan sahayoniyya guda hudu da gwamnatin Isra’ila ta karbe su tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da ta fara aiki kwanaki 34 da suka gabata.