Kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Ba zata gabatar da martaninta kan matsayin cimma yarjejeniyar da ake yi da ita ba saboda gwamnatin ‘yan shayoniyya ba ta gabatar da taswirar janyewa daga Gaza ba
Wata majiya da ke kusa da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a jiya Talata ta bayyana cewa: Har yanzu kungiyar Hamas ba ta mika martaninta ga daftarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Zirin Gaza ba, saboda har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta gabatar da taswirorin da zata bi wajen janyewa daga yankunan da take cikin na Falasdinawa ba.
Majiyar ta kara da cewa: Wadannan taswirorin sun hada da janyewar daga layin Netzarim domin tabbatar da amincin mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, da janyewar daga kan iyakar Philadelphi da ke kan iyaka da kasar Masar, da kuma janyewar daga Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza gami da birnin Rafah dake kudancin Zirin na Gaza.