Kungiyar Hamas Ta Godewa Kasashen Duniya Wadanda Suka Ki Amincewa Da Shirin Trump Na Korarsu Daga Gaza

Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai

Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa. Mutanen gaza basa son rabuwa da kasarsu, ta kaka da kakanni. Kuma suna maraba da dukkan shawarorin da kasashe larabawa da sauran kasashe duniya zasu bayar, don ganin  an sake gina Gaza ba tare da an kori falasdinawa daga kasarsu ba.

A wani Labari kuma shugaban kasar Amurka ya bawa falasdinawa a Gaza nan da ranar Asabar mai zuwa, na su saki dukkan yahudawan da suka rage a hannunsu ko kuma aka kawo karshen tsagaita wuta tsakaninsu da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments