Kungiyar Hamas Ta Bukaci Al’ummar Duniya Ta Goyi Bayan Al’ummar Falasdinu Kan Batun Neman Korarsu Daga Kasarsu

Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da

Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a duk fadin duniya da su fito domin gudanar da gagarumar zanga-zanga da tarukan goyon bayan al’ummar Falasdinu gami da hadin gwiwa a dukkanin birane da wuraren taruwar duniya, domin jaddada yin watsi da yin Allah wadai da shirin korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Laraba ta ce: Ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi masu zuwa su kasance wani yunkuri na duniya, inda ake za a daga muryoyi masu karfi domin nuna adawa shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira da korarsu daga muhallinsu, wanda ‘yan mamaya da magoya bayansu suke kiran a taimaka musu wajen cimma wannan mummunar manufa.

Hams ta jaddada cewa: Wannan zanga-zangar suna zuwa ne domin nuna goyon baya ga haƙƙin da al’ummar Falasdinawa suke da shi na kare ƙasarsu, daga ciki kuwa har da ‘yancinsu, ‘yancin kai, hakkin tsara makomarsu da kubutar da kasarsu daga hadamar ‘yan mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments