A cikin wata sanarwa da Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta fitar ta jaddada cewa tana ci gaba da sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya, tana mai jaddada wajibcin mutunta hadin kai da ‘yancin kai da kuma amincin Jamhuriyar Larabawa ta Siriya.
Wannan dai ya fito ne daga bakin Jamal Rushdi, mai magana da yawun babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, wanda kuma ya bayyana damuwar Ahmed Aboul Gheit, babban sakataren kungiyar dangane da ci gaba da samun bullar rikici da tashe-tashen hankula a kasar Siriya, inda rikicin ya fi shafar fararen hula, sakamakon sake bullar kungiyoyin ‘yan ta’adda da nufin mamaye wasu yankunan kasar.
Kakakin kungiyar ta kasashen Larabawa ya jaddada aniyar babban sakatariyar kungiyar ta daukan duk wani batu na siyasa domin warware shi ta hanyar lumana a kasar Siriya, kamar yadda yake kunshe a cikin shawarwarin da kwamitin kungiyar ya gabatar a matakai daban-daban.