Kungiyar Guinness Ta Rigistan Ayyukan Bajinta Ta Duniya Ta Dakatar Da Karban Daga HKI

Hukuma ko kungiyar ‘The Guinness World Records organization’ ta bada sanarwan cewa daga yanzu ta daina karban duk wata bajinta ko wani al-amiri da ya

Hukuma ko kungiyar ‘The Guinness World Records organization’ ta bada sanarwan cewa daga yanzu ta daina karban duk wata bajinta ko wani al-amiri da ya shafeta daga HKI saboda ta’asan da take aikatawa a Gaza, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun tabbatar da cewa, kissan kare dangine.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran ya bayyana cewa kafin haka kungiyoyin kasa da kasa da dama da kuma fitattun mutanen sun tabbatar da cewa abinda HKI take aikatawa a Gaza laifukan yaki ne, don haka haramcin hukumar Guinness na karban duk wata bajinta daga HKI ya zo ne don ya tabbatar da abinda hukumomin da suka gabaceta suka yi.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya zuwa yanzun sojojin HKI sun kashe Falasdinawa kimani dubu 70,000 sannan wasu dubu 171 kuma suka jikata a yayinda wasu kimani dubu 10 kuma suka bace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments