Kungiyar Da’ish Ko IS Ta Kai Harin Kunan Bakin Wake A Masallacin Juma’a Na ‘Yan Shi’a A Pakistan

Kungiyar Da’ish ta dauki alhakin kai hari a masallacin Islamabad, inda ta kashe mutane tare da jikkata wasu da dama Kungiyar Da’ish ko IS ta

Kungiyar Da’ish ta dauki alhakin kai hari a masallacin Islamabad, inda ta kashe mutane tare da jikkata wasu da dama

Kungiyar Da’ish ko IS ta dauki alhakin harin da aka kai wa wani masallacin ‘yan Shi’a a birnin Islamabad na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyar shahadan mutane da dama.

A ranar Juma’a, ‘yan sanda da jami’an gwamnati sun ce wani harin kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 31 tare da raunata kusan 170 lokacin da ya afka wa masallacin yayin sallah.

Majiyoyin tsaro na Pakistan sun ruwaito cewa wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ya yi jigida da shi a lokacin da aka tsayar da shi a kofar masallacin, wanda ke yankin Terlai a wajen birnin Islamabad.

Ministan Tsaron kasar Khawaja Asif ya rubuta a dandalin X cewa maharin ya tarwatsa kansa ne a layin masu ibada da ke shiga Masallacin.

Ya bayyana cewa maharin yana da tarihin tafiya zuwa Afghanistan kuma ya zargi makwabciyarsa Indiya da daukar nauyin harin, ba tare da bayar da shaida ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted