Kasashen kungiyar ‘ the Association of Southeast Asian Nations’ ko ASEAN ta yi allawadai da kisan kiyashiun da ke faruwa a zirin gaza, sannan ta bukaci kasashen duniya su dauki matakan da suka dace don dawo da doka da oda na kasar Falasdinu da aka mamaye, a kuma kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a can.
Har;ila yau kungiyar ta bukaci a bude kofofin shiga gaza don isarda abinci da magunguna zuwa zirin gaba sannan a daina kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. A wata sanarwan da da kungiyar ta bayar tace a dakatar da kashe fararen hula a dukkan bangarorin sannan ta bukaci a maida aikin hukumar UNURWA na MDD don isar da agaji a cikin gaza.