Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Nasarar Nguema A Zaben Shugaban Kasa

Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da

Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.%  da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara.

Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba.

Magoya bayan Nguema sun yi bikin  hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki.

Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin sake gina cibiyoyin gwamnatin kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Gabon dai kasa ce mai arzikin man fetur, sai dai kuma mafi yawancin mutanen kasar suna rayuwa a cikin talauci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments