Kenya Ta Sanar Da Taron Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka, Tare Da Tshisekedi Da Kagame

Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar

Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame.

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan tawayen M23 ke ci gaba da dannawa kan birnin Goma inda ake ta musayar wuta.

A cewar wasu majiyoyin MDD da na tsaro, sojojin Rwanda da mayakan M23 sun shiga birnin a ranar Lahadi, in ji kamfanin dillancin labaran Faransa.

Yakin da ake gwabzawa a kusa da Goma da kuma harbe-harbe da aka yi a birnin ya kuma sa mazauna babban birnin lardin ketare kan iyaka zuwa kasar Rwanda.

A wani labarin kuma sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya zargi gwamnatin Kigali kan sabon fadan da akeyi a gabashin DRC.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments