Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5

Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin

Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi ga fannin hakar ma’adinai na kasar.

Kamfanin ShantaGold Kenya Limited ya sanar da cewa, an gano hakan ne a hanyar Lerehanda, wanda ya ratsa cikin kananan hukumomin Kakamega da Fihiga, bayan kwashe tsawon shekaru ana bincike.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce aikin yana da nufin samun lasisin da ya dace don hakar albarkatun zinare a mahakar Isolo-Bushiangala don kasuwanci.

Ta kara da cewa hakan na iya bunkasa tattalin arzikin cikin gida ta hanyar samar da ayyukan yi, da kuma bayar da gagarumar gudunmuwa ga gwamnatin Kenya ta hanyar haraji da kuma kudaden shiga, wadanda ake ganin zai  iya kara hakaba  ci gaban tattalin arzikin gida da na yankin.

Ana sa ran gano sabbin ma’adanan  zai mayar da kasar Kenya ta zama babbar kasuwa a masana’antar zinari a gabashin Afirka.

Sanarwar kamfanin ta kara da cewa binciken ya hada da ma’adinai masu inganci da suka dace kasuwanci, kuma ana ci gaba da nazarin yiwuwar ci gaba da ayyukan hakarsu a  karkashin kasa.

Binciken ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bukatar zinariya a duniya, inda farashinsa ya yi tashin gwauron zabi a duniya saboda rashin tabbas na tattalin arziki.

Manazarta sun ce a nan gaba bangaren zinari na kasar Kenya zai iya taka muhimmiyar rawa wajen  jawo hankulan masu zuba jari da ke neman sabbin wuraren kasuwannin ma’adanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments