Search
Close this search box.

Kassam: Harin Da Mu Ka Kai A Rafah Yana Nuni Da Cin Kasar HKI A Gaban ‘Yan Gwagwarmaya

Dakarun ‘Kassam’ na  kungiyar Hamas, sun bayyana cewa; Harin da su ka kai a birnin Rafah dake kudancin Gaza, yana kara tabbatar da cin kasar

Dakarun ‘Kassam’ na  kungiyar Hamas, sun bayyana cewa; Harin da su ka kai a birnin Rafah dake kudancin Gaza, yana kara tabbatar da cin kasar sojojin Isra’ila, tare da yin aikawalin wasu sabbin hare-haren.

Kamfanin dillancin labarun Turkiya ya Ambato kakakin dakarun na ” “Kassam” Abu Uabdha yana cewa; Hari mai sarkakiya mu ka kai a ranar Asabar dfin nan, manuniya ce akan cin kasar makiya wajen fuskantar gwagwarmayarmu,kuma wani duka ne mai zafi ga sojijinsu.”

 Abu Uabidah ya kuma ce; za mu cigaba da kai hare-hare masu tsanani ga makiya a duk inda suke, kuma sojojin mamayar za su rika cin karo da kwanton bauna na mutuwa a ko’ina.

Wannan sanarwar da ta fito daga Abu Ubaidah dai ta zo ne, bayan da ‘yan sahayoniyar su ka yi furuci da cewa an halaka musu sojoji 8 bayan wani hari da aka kai wa motarsu mai sulke a sansanin “Tal-Sultan”.

Sanarwar ‘yan sahayoniyar ta kuma bayyana cewa ya zuwa adadin sojojinsu da aka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba, sun kai 658, wasu 306 daga cikinsu a filin daga wacce ta fara daga raanr 27 ga watan na Oktoba na shekarar da ta gabata.

Su kuwa sojojin sahayoniya da su ka jikkata a wannan tsakanin sun kai 3000 da 835,1936 daga cikinsu a filin daga.

Har yanzu dai sojojin na HKI suna cigaba da tafka laifukan yaki akan al’ummar Falasdinu, musamman ma dai a yankin Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments