Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi.
Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.”
Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu.
A nashi gefen ministan harkokin wajen Iran ya ce; Shirin na Donald Trump na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza, ci gaba ne na tsohon shirin ‘yan mulkin mallaka na shafe hakkokin Falasdianwa, tare da yin kira da a dauki matakin fuskantar wannan makarkashiya.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya yi tir da furucin Benjemin Netanyahu dake cewa a kafa kasar Falasdinu a cikin Saudiyya, tare da cewa wannan Magana ce ta dagawa da girman kai na ‘yan mamaya.