Search
Close this search box.

Kasashen Qatar, Saudiyya Da Kuwait Sun Nuna Halin Damuwa Da Alhimi Kan Hatsarin Jirgin Shugaban Iran

Kasashen Qatar, Saudiyya da Kuwait sun nuna halin damuwa tare da alhininsu kan hadarin jirgin shugaban kasar Iran Kasashen Qatar, Saudiyya da Kuwaiti sun bayyana

Kasashen Qatar, Saudiyya da Kuwait sun nuna halin damuwa tare da alhininsu kan hadarin jirgin shugaban kasar Iran

Kasashen Qatar, Saudiyya da Kuwaiti sun bayyana alhininsu ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan hadarin jirgin saman shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi a yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga bikin bude madatsar ruwa ta hadin gwiwa a kan iyakar kasar Iran da Azerbaijan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majid Al-Ansari ya bayyana cewa: Kasar Qatar a shirye take ta bayar da duk wani nau’i na taimako wajen neman jirgin shugaban kasar Iran tare da bayyana matukar damuwar kasar ta Qatar game da makomar jirgin shugaban kasar Iran mai saukar ungulu da ta yi hatsari. Al-Ansari ya kara da cewa: Suna bayyana fatan samun lafiya ga shugaban kasar Iran da ministan harkokin wajen kasar da kuma tawagarsu.

A nashi bangaren, ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya ce: Suna cikin matukar damuwa da abin da ake yadawa a kafafen yada labarai dangane da jirgin shugaban kasar Iran mai saukar ungulu. Don haka suna tabbatar da cewa: Masarautar Saudiyya tana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da take ‘yar uwa, a cikin wannan yanayi mai wuyar gaske, tare da jaddada cewa: Saudiyya tana tabbatar da shirinta na ba da duk wani taimako da hukumomin Iran ke bukata.

A nata bangaren, ma’aikatar harkokin wajen Kuwait ta sanar da cewa tana ci gaba da bibiyar labaran da suke fitowa dangane da jirgin saman shugaban kasar Iran da tawagarsa tare da goyon bayan Iran, tana mai bayyana fatan kasar Kuwait na neman lafiyar shugaban kasar Iran da tawagarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments