Kasashen Mali, Burkina Faso Da Nijar Sun Daukewa ‘Yan Kasashen Ecowas Karbar Biza

Kasashen 3 da su ka kafa kawance na tsarin Kwanfadaraliyya sun sanar da ficewa daga cikin kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afika “Ecowas” a ranar

Kasashen 3 da su ka kafa kawance na tsarin Kwanfadaraliyya sun sanar da ficewa daga cikin kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afika “Ecowas” a ranar 15 ga watan Janairu na wannan shekara mai karewa.

Daukar wannan matakin ya biyo bayan dakatar da kasashen uku da aka yi daga cikin kungiyar ta “Ecowas’ mai mambobi 15. Bugu da kari sun zargi kungiyar da cewa ta zama wani makami a hannun ‘yan mulkin mallaka, musamman ma dai Faransa.

A halin yanzu dai kungiyar ta Ecowas tana  gudanar da taro a birnin Abuja domin tattauna  da dama da su ka hada wannan matakin da kasashen uku su ka dauka.

Ana hasashen cewa ficewar kasashen daga Ecowas da jumillar mutanenta ya kai miliyan 72, zai yi tasiri a cikin harkokin tattalin arzikin yankin.

Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdullahi Diop ne ya karanta bayanin daukewa mutanen  kasashen na Ecowas neman izinin shiga cikinsu na Visa. A bayanin nashi ya ce; “Kasashen kwanfedaraliya na yankin Sahel sun  yanke cewa ‘ya’yan kasashen kungiyar  Ecowas, ba su bukatar izinin shiga na visa.”

Bayanin ya biyo bayan sa’o’i uku da kasashen uku su ka sake nanata cewa, babu ja da baya akan matsayar da su ka dauka na raba hannun riga da kungiyar Ecowas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments