Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.”
Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce harin, ha’inci ne da wauta.”
Sakatare-Janar na Kungiyar ya bayyana “cikakken goyon baya” ga Qatar bayan abin da ya kira “cin zarafin Isra’ila”, yana mai jaddada cewa dole ne kasashen duniya su dauki kwakkwaran mataki kan Tel Aviv.
Shi ma da yake jawabi a taron share fagen kasashen musulmin da na Larabawa, firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya yi tir da harin da ya danganta da na “ta’addancin kasa” da kuma keta duk wani yunkuri na shiga tsakani.”
Sheikh Abdulrahman Al Thani ya bukaci kasashen duniya da su daina yin Magana mai tamkar harshen damo, su kuma hukunta Isra’ila saboda “laifin” da ta aikata.
Ya yi wannan jawabi ne a wani taron share fage da aka yi a jajibirin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci da Qatar ta shirya bayan da Isra’ila ta kai wani hari irinsa na farko kan kasar a kan shugabannin Hamas a Doha. Yau Litinin ne shugabannin kasashen na Larabawa da na Musulmi zasu hadu a birnin Doha domin tattauna batun.