Gwamnatocin kasar Ireland, Espanita da kuma Norway sun bada sanarwan a hukumance na amincewa da kasar Falasdinu a matsayin cikekkiyar kasa mai zaman kanta, sun kuma yi kira ga sauran kasashen duniya su bi sawunsu.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta nakalto firai ministan kasar Noeway Jonas Gahr Store ya bayyana cewa amincewa da kasar Falasdinu shi ne kawai hanyar samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Kuma abinda HKI take yi a gaza barazana ce ga hanyar tabbatar da zaman lafiya wanda ya amince da kasashen biyu.
Sai dai sojojin HKI sun ci gaba kisan kiyashi a yankin gaza a dai dai lokacinda Falasdinawa suke maraba da matakan da kasashen uku suka dauka na amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta.
Kamar yadda ake tsammani dai, gwamnatin HKI ta yi allawadai da wadannan kasashen turai uku, wato Norway, Espania da kuma Ireland da amincewa da Kasar Palasdinu mai cikekken yanci. Ta kuma kara da cewa zata janye jakadunta daga wadannan kasashe.
A garin Rafa kuma sojojin yahudawan sun ci gaba da kissan kiyashin da sukewa Falasdinawa, inda falasdina kimani 80 suka yi shahada a wurare daban daban a yankin .