Kasashen Iran Da Tunisya Suna Shirin Bunkasa Alaka A Fagagen Yawon Bude Ido

Minista mai kula da al’adu da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad

Minista mai kula da al’adu da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmanci.

Kamfanin dillancin labarun “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunisiya ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Larabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude ido mabanbanta da su ka hada da na tarihi da kuma na dabi’a, sannan ya kara da cewa: Iran din tana da cibiyoyi na karbar bakuncin masu zuwa yawon bude ido.

A nashi gefen, Imad al-Rahmani ya bayyana muhimmancin alakar dake tsakanin kasashen biyu yana mai kara da cewa: “Tarayyar da kasashen biyu su ka yi a cikin al’adu za su iya share fage na yin aiki tare mai dorewa, kuma samar da zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen biyu kai tsaye za ta taimaka wajen bunkasa wannan alakar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments