Kasashen Gabashi Da Kudancin Afrika Zasuyi Taro Kan Rikicin Gabashin Kongo

Kasar Kenya mai rike da shugabancin kungiyar kasashen gabashin Afirka ta EAC, ta sanar cewa za’a gudanar da wani taron hadin gwiwa da kungiyar raya

Kasar Kenya mai rike da shugabancin kungiyar kasashen gabashin Afirka ta EAC, ta sanar cewa za’a gudanar da wani taron hadin gwiwa da kungiyar raya kasashen yankin kudancin Afirka ta SADC a ranar Juma’a a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania.

Taron na kwanani biyu zai samu halartar shugabannin kasashen Rwanda da Kongo, Paul Kagame da Félix Tshisekedi.

Al’amura sun dagule a yankin na gabshin Kongo bayan harin da ‘yan tawayen M23 – da Rwanda ke marawa baya suka kai a Goma, babban birnin Kivu ta Arewa, a makon jiya, da kuma fadan baya-bayan nan a Kudancin Kivu.

A cikin ‘yan kwanakin nan, kungiyoyin biyu da ke da ra’ayi daban-daban kan yadda za a warware rikicin, sun bayyana fatan shirya taron hadin gwiwa na gaggawa domin daidaita matsayarsu da kuma kaucewa hadarin da ke tattare da rikicin yankin. “

Manufar wannan babban taron it ace ci gaba da kokarin “sake tuntuba ta diflomasiyya don kawo karshen tarzomar” a gabashin DRC.

A wani labarin kuma Kwamitin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taro cikin gaggawa a ranar Juma’a domin duba rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da kuma tasirinsa kan ‘yancin bil’adama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments