Kasashen EU3 Sun Ce, Dauke Takunkuman Tattalin Arzikin Wa Kasar Iran Ya Fi Karfinsu

Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta

Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar.

Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata.

Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran ta ke da sarkakiya. Ya kuma kara da cewa hukumar makamashin nukliya ta duniya ce yakamata ta kare hakkin duk wata ka a duniya kan hakkin mallakan fasahar nukliyan ta zaman lafiya.

Shugaban hukumar  makamashin nukliya ya bayyana cewa, har yanzun yarjeniyar JCPOA tana raye, amma iran zata maida hankali a kanta ne kawai idan dayan bangaren ya dawo kan ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments