Kasar Yemen ta haramta fitar da man da Amurka ke fitarwa a matsayin mayar da martani ga wuce gona da irin sojojin Amurka kan kasarta
Cibiyar kula da ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a na kasar Yemen ta sanar da dakatar da fitar da mai da Amurka ke fitarwa daga ranar 17 ga watan Mayu, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.
Cibiyar daidaita ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a ta sanar a safiyar ranar Asabar, matakin hana fitar da danyen mai da Amurka ke yi daga cibiyoyin man fetur na kasar, wanda zai fara aiki daga ranar 17 ga watan Mayun wannan shekara ta 2025.
Wannan shawarar dai ta zo ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kan fararen hula da ababen more rayuwa a Yemen. A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta ce: Kamfanonin da suka karya dokar, za a sanya su cikin jerin wadanda aka kakaba musu takunkumin da aka sanyawa masu ta’addanci kan kasar Yemen.