Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin Gaza bai da wata dangantka da tsagaita bude wuta.
Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ya nakalto Yerima Faisal bin Farhan yana fadar haka a jiya Jumma’a.. Ya kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya su takurawa HKI ta bada dama a shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin gaza saboda ceton mutanen yankin daga yunwa mai tsanani da suke fama da shi.
Ministan yana magana ne bayan taron ministocin harkokin waje na kasashen larabawa da Musulmi a Antalya, inda suka tattauna batun yadda al-amura suke a zikin gaza da ya hanyoyin da za’a bi don tsagaita wuta da kuma shigo da kayakin agazaji cikin yankin da gaggawa.
Yerema faisal ya kamma da cewa kasashen larabawa da musulmi basa son duk wani shiri nakorar Falasdinawa daga Gaza, kuma suna goyon bayan shawarorin da kasashen Qatar da Masar suka gabatar dangane da tsagaita wuta a gazar.