A cikin wani taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar yayi a birnin Doha Majeed Al-ansari ya fadi cewa Qatar na ci gaba da bibiyar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin isra’ila da hamas kuma tana kokarin hana duk abin da zai Sanya yarjejeniyar ta rushe.
Ya kare da cewa mataken da isra’ila ke dauka yana matukar barazana ga yajejeniyar da yasa take tangal-tangal.
Wannan itace yarjejeniyar mafi tsawo da aka cimma daga lokacin da israila ta fara kisan kare dangi zuwa yau, kusan shekaru biyu ke nan , yace yanzu haka ana kokarin ganin an shiga mataki na biyu na yarjejeniyar da aka kulla na dakatar da bude wuta,
Matakin farko na yajejeniyar da aka kira ta zaman lafiya kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya fitar, kungiyar hama za ta saki dukkan mutane 48 da take rike da su 20 daga cikin wadanda suke da rai, kuma kungiyar hamas da sauran kungiyoyin falasdinawa sun aiki da alkawarin da suka dauka
Mataki na 2 na yarjejeniyar shi ne isra’ila za ta janye daga yankunan da ta mamaye a cikin Gaza, kana akafa gwamnatin rikon kwaryar da za ta jagorancin yanki, sai kuma a aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa