Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.   A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke  shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar Diblomasiyya da HKI ba.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakisatn ta bayyana cewa, kafafen yada labarai da dama sun watsa labaran cewa kasar ta Canza matsayinta dangane da kudurin hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da rikicin nag abas ta tsakiya, ta kuma kara da cewa wannan labarin ba gaskiya bane. Saboda kasar Pakistan tana tare da kungiyar OIC dangane da goyon bayan al-ummar Falasdinu. Don haka Pakisatan bata amincea da samuwar HKI ba. Har’ila yau majalisar kasa ta kasar Pakisatn ta amince da babban rinjaye ko kuma gaba dayan yan majalisar da rashin amincea da HKI da kuma goyon bayan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments