Ministan Harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya fara ayyukan diblomasiyya inda ya fara tattaunawa da Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi dangane da farfado da tattaunawa kan shirin Iran na makamashin Nukliya tare da shugaban hukumar, IAEA Rafael Grossi, da kum wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff,. Amma a yanzun ba tare da barazana ko kuma kaiwa hare-hare ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wadannan bangarori biyu suna son Iran ta sake bada wata dama, don tattauna batun shiruin makamashin nukliya na kasar da kuma dangane da tashe tashen hankula a yankin yammacin Asia.
A dai dai lokacinda al-amura suke ci gaba da tarbarbarewa a yankin kasar masar ta sanya kanta a matsayin mai shiga tsakanin Iran da wadannan kasashen yamma.
Ministan harkokin wajen Iran yace a halin yannzu kuma bama dogaro da maganar Amurka don a sanda suka kaimana hare-hare bas u gaya mana ba.