A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab.
Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim Herzog daga Lambun shakatawa,saboda matsin lambar kungiyoyin da suke goyon bayan Falasdinawa.
Jaridar ta ce sauya sunan wannan lambun yana da alaka ne da yakin Gaza, kuma an amince da shawarar da aka bijiro da ita a hukumar birnin ta hanyar kada kuri’u mafi rinjaye.
Wasu kungiyoyin da suke nuna goyon bayansu ga “Isra’ila” sun nuna rashin jin dadinsu da wannan matakin na sauya sunan lambun a birnin Dublin.
Lambun da aka sauya sunansa yaka kusa da wasu makarantu ne biyu na yahudawa na Firamare da sakandire da su kadai ake da su a Ireland. An bude lambun ne dai a karon farko a 1985 da sunan Oril Kowir Park’ sai dai daga baya an sa masa sunan shugaban Haramtacciyar Kasar Isra’ila na shida ” Chaim Herzog.