Jami’in tsaron kasar Iran ya karyata sabuwar da’awar jaridar New York Times ta kasar Amurka
Jami’in tsaron kasar Iran ya musanta wasu sabbin zarge-zargen da jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa game da zargin Iran cewa tana bunkasa ayyukannta na kera makaman kare dangi.
Jami’in tsaron ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Tasnim cewa: Ikirarin da jaridar New York Times ta yi game da wata kungiyar asiri ta masana kimiyyar Iran da ke aikin samar da hanyoyin kera makaman nukiliya cikin sauri, ba komai ba ne illa shirme da zage-zage marasa tushe da kan gado.
Jami’in ya kara da cewa: “Wadannan rudun tunani ba su da alaka da gaskiya, kuma kawai labaran karya ne da wasu kafafen yada labarai na Amurka ke yi don goyon bayan ajandar fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya Benjamin Netanyahu.”