Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi kakkausar suka kan kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suka yi a garin Al-Mawasi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya yi kira ga cibiyoyin kasa da kasa musamman ma Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakai masu inganci cikin gaggawa don dakile laifuffukan yahudawan sahayoniyya marasa iyaka kamar yadda tsarin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa suka tanada.
Kan’ani yayi kakkausar suka kan mummunan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tantunan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke birnin Khan Yunus a kudancin Zirin Gaza, wanda ya kai ga wani mummunan kisan kiyashi da ya lashe rayukan fararen hula Falasdinawa da dama.
Yayi ishara da cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi amfani da manyan makamai masu linzami wajen kai farmaki kan tantunan ‘yan gudun hijirar, lamarin da ya kai ga bacewar daukacin iyalai a cikin yashin ramin da wannan harin bam ya haifar, Kan’ani ya ganin cewa gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya ta hanyar hare-harenta na dabbanci kan fararen hulan Falasdinawa da tantunan ‘yan gudun hijirar, ta sake nuna cewa ba ta bin duk wani ka’idoji na dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin da’a da na jin kai.