Ministan harkokin wajen Iran ya yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suke kai wa kan kasar Yemen
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi la’akari da hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya da ‘yan sahayoniyya suka kaddamar kan ababen more rayuwa na kasar Yemen a matsayin cin zarafi ga ‘yancin kan kasar ta Yemen, da kuma keta hurumin dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin ganawarsa da manzo na musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen Hans Grundberg, ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan rawar da Majalisar Dinkin Duniya take takawa, da kokarin kyautata halin da ake ciki a kasar Yemen.
Araghchi yayi ishara da hare-hare ta sama da Amurka da Britaniya da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan ababen more rayuwa na kasar Yemen, ya kuma dauki wadannan hare-hare a matsayin cin zarafi ga ‘yancin kai na kasar Yemen, da kuma keta dokokin kasa da kasa gami da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.