Kasar Iran Ta Bayyana Shirinta Na Mayar Da Martani Ga Duk Wata Barazana Kanta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta Kakakin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar kasa, kuma tana shirye ta gudanar da kumajin siyasa da diflomasiyya wajen kare muradunta da tsaron kasa, sannan tana da azamar daukan duk wani matakin kare kanta da masalaharta tare da mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin daka da gwagwarmayarta.

Isma’il Baqa’i ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga tambayar cewa; Maganganun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan dangane da Iran, inda ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi kan Iran cewa tana yunkurin kera makaman kare dangi, kawai da’awar karya ce tsagwaranta. Sannan Iran din ta tabbatar da karce-karyacensu sau da dama, kuma duk wanda ya nemi tabbas kan wannan lamari zai iya samun cikin sauki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments