Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin kasashen biyu masu karfin nukiliya.
Gwamnatin Indiya ta kai hare-hare da makamai masu linzami guda uku kan wasu wurare a yankin Kashmir da Punjab na kasar Pakistan, yayin da daya daga cikin makaman ya afkawa tsohon filin jirgin sama na Muzaffarabad a yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.
A nata bangaren, gwamnatin Indiya ta sanar da cewa ta kaddamar da wani farmaki kan abin da ta kira ababen more rayuwa na ‘yan ta’adda a Pakistan da Jammu da Kashmir, ta kuma ce sojojinta sun kai hare-hare kan wasu wurare 9 na Pakistan.
Indiya ta kara da cewa: Hare-haren sun fi mayar da hankali zuwa wasu wurare da aka tantance, kuma ba tare da nufin janyo wani tashin hankali ba, don haka ba a kai hare-haren kan wasu cibiyoyin sojin Pakistan ba.