Firai ministan kasar Beljium Bart De Wever ya fadawa sauran tokororinsa na kasashen turai kan cewa bai amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka kwace a kasashen turai don yakar kasar a Ukraine ba, sai tare da wasu sharudda.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wever ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa dokokin kasa da kasa sun hana a kwace kudaden wata kasa mai cikekken yenci, don wata bukata.
Kafin haka dai kasashen turai da dama sun gabatar da shawarar kwace dalar Amurka bil;iyon $229 na kudaden ruwan da kadarorin kasar Rasha da ke turai suka samar don yakarta a kasar Ukraine, wannan duk da cewa dokokin kasa da kasa sun haramta yin hakan.
Kasar Rasha dai tana da kadarori wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka billiyon $300 wadanda aka kwace a kasashen yamma bayan fara yaki a kasar Ukraine, Euro billion 210 suna kasashen turai.
Kasashen turai sun bukaci a bawa kasar Ukrain Euro Billion 180 daga cikinsu a matsayin bashi, wanda babu kudaden ruwa a cikinsu.
Firay ministan Beljium yana ganin yin haka wata cacace. Wata babban rikici ne wanda ba’a san yadda za’a warwareta nan gaba ba. Wannan ya nuna cewa akwai sabani mai tsanani tsakanin kasashen na turai dangane da wannan shirin.