Kasar Afirka ta Kudu tana shirin mika wasu karin cikakkun shaidu ga kotun kasa da kasa manyan laifuka haramtacciyar kasar Isra’ila
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana aniyar kasarsa na gabatar da karin wasu sabbin shaidu kan batun kisan kare dangi kan Falasdinawa a shari’ar da aka shigar a gaban kotun kasa da kasa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da shugaban kasar Afirka ta Kudu ya fitar a wannan mako ya bayyana cewa: A daidai lokacin da ake cika shekara guda da fara yakin kisan kare dangi a Gaza, kasarsa za ta gabatar da wasu sabbin shaidu ga kotun duniya kan muggan laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da tafkawa kan Falasdinawa.
Shugaban ya jaddada cewa: Takardun da kasarsa za ta mika wa “Kotun kasa da kasa” sun kunshi cikakkun shaidu da suke tabbatar da cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza.