An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa.
Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum.
Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa.
Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan.
Su kuwa matukan motocin Tasi (SYNCTAXITU), cewa su ka yi, ya kamata gwamnati ta kara yawan man fetur da ake hakowa a kowace rana.
Babban sakataren kungiyar matuka Tasi din Agali Ibrahim cewa ya yi, “ Idan aka fada mana cewa da akwai manyan motocin jigilar man fetur 25 da ake bai wa birnin Niamey, to abinda zan fada musu shi ne cewa bai isa ba.”
Haka nan kuma ya yi ishara da fasakwaurin man fetur din da ake yi da yana daga cikin dalilin karancinsa da ake fuskanta.
Da akwai shirin kara yawan tankokin mai daga 25 zuwa 100 da za a rika bai wa babban birnin ka kowace rana.
Ba kasafai ake shiga irin wannan yanayin ba a jamhuriyar Nijar wacce take da arzikin mamn fetur da aka fara hako shi tun a wajajen 2011.