Kamfanonin Inshora Jiragen Ruwa Sun Yanke Hulda Da Isra’ila Saboda Matsalar Hare-Haren Kasar Yemen

Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da

Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen

Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda suka kai ga nutsewa, a teku a ranar Alhamis.

A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya bayyana cewa: Majiyoyin masana’antar inshora sun ce “kamfanonin inshora za su yi kokarin kauce wa rufe duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ko da kuwa alakar a kaikaice ne.”

Kamfanin dillancin na Reuters ya nakalto daga Munro Anderson babban jami’in gudanarwa a Vessel Protect, wani kamfanin inshorar haɗarin ruwa na teku cewa: “Abin da suka gani a wannan makon yana kama da komawa ga ka’idojin kai hari a tsakiyar shekara ta 2024, wanda a zahiri ya haɗa da duk wani jirgin ruwa ko da kuwa yana da alaƙa mai nisa da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted