Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.”
Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira ” Nuna wariya ta kabilanci.”
Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.”
A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%.
Shi dai Chiroma ya bayyana cewa shi ne wanda ya lashe zaben, illa iyaka mahukuntan kasar sun yi magudi ne da sauya alkaluman kuri’un da aka kada.
Wani rahoto na MDD ya ce; Jami’an tsaron kasar Kamaru sun kashe masu Zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben 48, yayin da mahukuntan kasar suke cewa mutane 5 ne su ka rasa rayukansu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban kasa, inda ya yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake yi.
A karshen sakon nasa, Chiroma ya ce idan har ba a yi aiki da bukatar da ya bijiro da ita ba, to kuwa mutanen kasar za su yi duk abinda za su iya domin kwato da ‘ya’yansu da ake tsare da su.