Kalibof Yace: Iran Zata Maida Martani Mai Tsanani Kan HKI Idan Ta Sake Bude Yaki da Iran

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof  ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof  ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki da JMI, sannan sai sun yi nadamar fara yakin kamar yaki da kwanaki 12.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake gabatar da jawabi a taron tunawa da kuma yin addu’a ga shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kawowa kasar.

Ya ce HKI ba zata jurewa yaki mai tsawon lokaci ba, saboda Iran ta fi karfinsu, sannan wannan ne yasa gwamnatin Amurka ta shiga yakin, inda ta takaita da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar a fordo da Natanz da kuma Esfahan.

Daga karshe shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran ya bayyana cewa duk wata karawa da HKI zata kasance mai murkusheta ne , ta yadda ba zata sake tashi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments