Kakakin Sojan Iran: Za Mu Dankwafe Duk Wani Tsoma Bakin Amurka A Wannan Yankin

Mai Magana da yawun sojan jamhuriyar musulunci ta Iran Muhammad Ikrami Niya, ya fada a yau Alhamis cewa; Manufar Iran da babu tantama akanta shi

Mai Magana da yawun sojan jamhuriyar musulunci ta Iran Muhammad Ikrami Niya, ya fada a yau Alhamis cewa; Manufar Iran da babu tantama akanta shi ne shimfida ikonta akan mashigar Hurmuz, kuma za mu gwgawarmaya akan hakan har zuwa karshe.

Haka nan kuma ya kara da cewa; Amurkawa suna tsammanin cewa za su iya shimfida ikonsu akan mashigar ruwan Hurmuz,ta hanyar kai hare-hare akan wasu sansanoninmu da suke a gabar ruwan a kudancin kasar. Sai dai ba su san cewa jamhuriyar musulunci ta Iran za iya amfani da makaman da take da su daga kowace kusurwa ta kasar domin ci gaba da iko da mashigar.

Kakakin sojan ya kuma yi Ishara da yadda wasu kasashen wannan yankin su ka bai wa Amurka kasarsu ta girke sojoji da makamai, amma a halin yanzu su ne suke asara ta fuskar kasuwanci da tsaro.

Haka nan kuma ya ce, duk wani tsaro da za a shigo da shi daga waje ba mai dawwama ba ne, domin tsaro na hakika yana tabbata ne idan kasashen yankin su ka samarwa da kawukansu tsaro.

Kakakin rundunar sojan na Iran ya kuma ce matukar Amurkan ta ci gaba da yin abinda yake yi, to kuwa jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da kayan aikin da har yanzu ba ta fara amfani da su ba, za kuma ta iya yin tasiri a cikin yanayin wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted