Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran ba ko kuma ci gaban shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Iran a yammacin ranar Talata, Baqa’i ya yi la’akari da dukkanin rahotanni da kudurorin da suka shafi siyasa. Ya kuma kara da cewa Iran ba ta keta hurumin da ya rataya a wuyanta ba, kuma kasashen yammacin turai suna dora barazanarsu ne kan zargin da aka shafe shekaru 20 ana yi. Ya jaddada cewa Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na inganta sinadarin Uranium ba.
Ya yi nuni da cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, Rafa’el Grossi, yana aiki ne da son zuciya, da kuma maimaita labaran bangarorin da ke adawa da Iran, ya kara da cewa, mayar da “hanyar tayar da hankali” za ta fuskanci martani mai karfi na Iran.
Dangane da matsayin Sanya batun Iran a gaba a hukumar ta IAEA da kuma barazanar da kasashen Turai ke yi na fitar da wani kuduri a taron majalisar alkalan hukumar IAEA da ke gudana a halin yanzu, ya bayyana cewa, batun nukiliyar Iran wani kuduri ne na siyasa kawai tun da farko, a lokacin da ya shiga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kafin nan, lokacin da ake kallon lamarin a matsayin wani lamari mai yaduwa.