Kais Saied : Tunisia na goyon bayan gwagwarmayar al’ummomin Falastinu da Lebanon

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya tabbatar a wannan Talata cewa kasarsa na tare da  gwagwarmaya da tsayin daka na  al’ummar Palasdinu da Lebanon, yana

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya tabbatar a wannan Talata cewa kasarsa na tare da  gwagwarmaya da tsayin daka na  al’ummar Palasdinu da Lebanon, yana mai jaddada cewa mu’amala da ‘yan mamaya babban cin amana ne ga Falasdinawa.

Saeed ya bayyana a cikin jawabin nasa cewa: “Muna tare da dukkanin al’ummomin da ake zalunta, mun agoyon bayan gwagwarmayar  Palastinu, har sai sun kafa kasarsu mai cin gashin kanta a kan dukkanin Falasdinu,” ya kara da cewa: “Muna kuma tsayawa ba tare da wani sharadi ba tare da al’ummar Lebanon .”

Ya ci gaba da cewa: “Dole ne kowa ya sani cewa, babu wani na daidaita alaka da ‘yan ta’adda masu aikata laifuka yahudawan sahyoniya, kuma duk wanda ya yi mu’amala da su yana cin amanar Falasdinawa ne.”

Tare da goyon bayan Amurka, Isra’ila ta fara yakin kisan kare dangi a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa sama da 42,600 tare da jikkata kimanin 100,000 yawancinsu yara da mata, sama da 10,000 sun bata babu duriyarsu.

A halin da ake ciki dai, hare-haren da yahudawan sahyuniya suka kai kan kasar Labanon ya yi sanadin shahar mutane 2,483 da kuma raunata kimanin 11,628 da suka hada da mata da kananan yara masu yawa, baya ga sama da mutane 1,340,000 da suka rasa matsugunansu. Yawancin wadanda abin ya shafa da kuma wadanda suka rasa matsugunansu an rubuta su ne tun ranar 23 ga Satumba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments